(ABNA24.com) Sarkin kasar Morokko Muhammad na VI ya tabbatar da cewa akwai rashin adalci da nuna bambanci a cikin tsarin tafiyar da kasar ta Morokko, sannan ya sha alwashin kawo karshen hakan a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto sarkin yana fadar haka a jiya Litinin a lokacinda yake jawabi a bikin cikarsa shekaru 20 da hawa kan kujerar sarautar kasar.
Banda haka sarkin ya nada Sa’aduddeen Al-Uthmani, wani mai kishin addini a matsayin sabon firai ministan kasar, tare da umurnin gabatar da sauye-sauye a harkokin gudanar da kasar, da kuma rage bambanci tsakanin masu hannu da shuni da kuma talakawan kasar a bangarorin tattalin da zamantakewa a kasar.
Har’ila yau Sarki Muhammad na VI ya yi afwa ga fursinoni 4,764 saboda zagayowan ranar da ya hau kan kujerar sarautar kasar shekaru 20 da suka gabata.
Daga cikin wadanda sarkin ya yi wa afwa, akwai wadanda aka kama a lokacin yunkurin mutanen yankin “Rif” na kasar a cikin watan Octoban shekara ta 2016, karkashin shugabancin Nasir Zafzafi inda suka bukaci gwamnatin kasar ta kyautata rayuwar mutanen yankin.
/129
31 Yuli 2019 - 04:07
Lambar labari: 965916
Sarkin kasar Morokko Muhammad na VI ya tabbatar da cewa akwai rashin adalci da nuna bambanci a cikin tsarin tafiyar da kasar ta Morokko, sannan ya sha alwashin kawo karshen hakan a kasar.